Wata sanarwa da kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka(IGAD) wadda ke shiga tsakanin tattaunawar ta bayar, ta bayyana cewa, za a fara tattaunawar ce da misalin karfe 5 na yamma agogon wurin.
Ana gudanar da tattaunawar ne,yayin da bangarorin biyu ke ikirarin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma,duk da rahotannin da ake samu cewa, ana gwabza fada tsakanin bangarorin biyu a sassan daban-daban na jaririyar kasar.
Sanarwar kungiyar ta IGAD na cewa,tattaunawar za ta hallara gwamnatin Sudan ta kudu da kungiyar adawa ta SPLM wuri guda
A makon da ya gabata ne aka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da nufin daidaita rikicin siyasar da ake fama da shi a kasar, tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar da aka tsige daga mukaminsa a watan Yulin shekarar 2013,kana aka zarge shi da yunkurin yin juyin mulki.
A ranar 15 ga watan Disamban shekara 2013 ne, rikici ya barke a tsakanin dakarun da ke goyon bayan wadannan jagorori biyu,lamarin da ya tilasta wa mutane sama da 870,000 kaura daga gidajensu kana da dama suka tsunduma cikin mawuyacin hali na neman agaji.(Ibrahim)