A cikin wata sanarwa ne, bankin ya bayyana cewa wannan shirin zai taimaka wa kasashen biyu na Afrika damar yin musanyar wutar lantarki. Baya ga wanna kuma, shirin makamashin tsakanin Tanzaniya da Kenya zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa dunkulewar shiyyar ta hanyar musanyar makamashi, in ji sanarwar.
Wannan shirin zai kara kyautata inganci, yawa da kuma saukin samun wutar lantarki a shiyyar gabashin Afrika, tare da taimakon musanyar makamashi mai tsabta tsakanin kasa da kasa da samun kasuwa mai kyau ta rarar makamashi zuwa wasu kasashe makwabta, in ji wannan sanarwa.
A zagayen farko, wannan shiri zai taimaka wa kasashen biyu wajen yin musanyar wutar lantarki, wanda kuma zai biyo baya tare da shige da ficen makamashi tsakanin kasashen dake hade da juna ta wannan fanni, a cewar wannan sanarwa. (Maman Ada)