A cikin wata sanarwar da ya bayar a ranar, shugaba Kenyatta ya ce, yana farin ciki sosai da wannan albishir na janye zargi kansa, kuma ya jaddada cewa ba shi da laifi ko guda.
Sannan ya bayyana cewa, kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ta bata dogon lokaci kan wata matsalar da ba ta da wani abin shaida a bayyane, wannan ya alamta cewa, haramtacciyar moriya na lalata da kuma rage amfanin dokokin kasa da kasa.
A shekarar 2012, kotun ICC ta zargi Uhuru Kenyatta da laifin keta hakkin dan Adam, amma shugaba Kenyatta ya cigaba da watsi da wannan zargi. A watan Oktoba na shekarar bana, ya halarci wani taron saurara da kotun ta shirya a Hague, kuma shi ne shugaba mai ci na farko a duniya da ya je kuma ya amsa karar kotun ICC da kansa. (Sanusi Chen)