Sanarwar wadda ke kunshe da sakon jaje ga iyalan wadanda harin ya ritsa da su, da ma gwamnatin kasar, da daukacin jama'arta, ta kuma jaddada aniyar MDD, ta goyon bayan kasar Kenya a yakin da take yi da ta'addanci. Kana ta yi fatan cimma nasarar kai wa ga tabbatar da tsaron rayukan al'umma bisa dokokin duniya da na kasar.
Rundunar 'yan sanda a Kenya dai ta ce wasu dakaru ne suka bude wuta kan wasu ma'aikatan dake fasa duwatsu, a yankin Mandera dake arewacin kasar ta Kenya, lamarin da ya haddasa rasuwar ma'aikatan a kalla 36.
'Yan sandan sun kuma zargi mayakan kungiyar Al-Shabaab na kasar Somaliya da aikata wannan ta'asa. (Zainab)