Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya ce aikin shimfida layin dogo da zai hada biranen Mombasa da Nairobi zai yi matukar taimakawa Kenya, wajen samun bunkasar tattalin arziki, tare da samar da dimbin guraben ayyukan yi ga jama'ar kasar.
Shugaba Kenyatta ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ganin yadda wannan aiki ke tafiya, aikin da kamfanin ginin hanyoyi da gadoji na kasar Sin gudanar da shi.
Shugaban kasar Kenyan ya kuma ce aikin, zai taimakawa tattalin arzikin kasar samun bunkasuwa daga kashi 5.8 bisa dari, zuwa kashi 8 bisa dari. Kaza lika zai samar da guraben ayyukan yi masu dimbin yawa, ya kuma taimakawa matakin da Kenyan ke dauka, na sauya matakan bunkasa tattalin arzikinta.
A nasa jawabi, ministan ma'aikatar sufurin kasar Michael Kamau, cewa ya yi da zarar aikin ya kammala, zai rage kudaden da ake kashewa a fannin dakon kayayyaki tsakanin biranen Mambasa da Narirobi, matakin da zai sanya kasar samun karin damar zuba jarin kasashen waje.
Rahotanni sun bayyana cewa, layin dogon mai tsawon kilomita 480, zai ratsa gundumomi 8 na kasar, kuma aikin zai lashe zunzurutun kudi har dala biliyan 3.8.
An dai kaddamar da aikin shimfida wannan layin dogo ne a ranar 1 ga watan Janairun nan, inda ake sa ran bayan kammalarsa, lokacin da ake shafewa a tafiya tsakanin biranen biyu zai ragu daga sa'o'i 10 zuwa sa'o'i 4.5. Kana aikin zai samar da fa'ida mai yawa ga Kenya da ma a dukkanin yankin gabashin Afrika. (Amina)