Mutane a kalla 12 aka ceto daga wani gini mai hawa 5 wanda ya ruguje a arewa maso gabashin birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya a daren ranar Lahadi 4 ga wata.
Hukumar ba da agaji ta Red Cross ta kasar Kenya wato KRCS da kungiyar taimako ta St. John Ambulance wadanda suka gudanar da aikin ceto cikin hadin gwiwa sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu an riga an ceci mutane a kalla 12 yayin da ake damuwa kan cewa, ba a san yawan mutanen suka bace ko suke karkashin tarkacen ginin da ya ruguje ba.
"A kalla an ceto mutane 12. Yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin ceto daga fannoni daban daban." a cewar Fred Majiwa, kakakin kungiyar taimako ta St. John Ambulance.
Har wa yau hukumar ba da agaji ta Red Cross ta kasar Kenya wato KRCS ta ce, ta kafa wani ofishin musamman domin taimakawa wadanda mambobin iyalansu suka bace.
Ginin da ya ruguje yana uguwar Huruma da ke arewa maso gabashin birnin Nairobi, hedkwatar kasar. (Tasallah)