Uwargidan Shugaban kasar Kenya, Margaret Kenyatta wadda ta bude taron a hukumance, ta shaida ma kwararrun kiwon lafiya mahalarta taron cewa fasahar sadarwa na zamani babban abu ne da zai iya magance matsalolin kiwon lafiya da dama wanda ya ke addabar nahiyar.
Madam Margaret Kenyetta don haka ta kalubalanci kwararrun a bangaren kiwon lafiya su zama masu tunanin abin da zai iya yiwuwa lokacin da suke kara nazarin hanyoyin samun mafita akan matsalolin da dama da suka addabi nahiyar musamman a bangaren da ya shafi haihuwa da makamancin haka.
Ta ce karuwan bukatu yanzu akan kiwon lafiya da kasancewa cikin koshin lafiya a ma'aikatun fasashar sadarwa na zamani ya bada dama mai kyau ga nahiyar ta kara zurfafa yadda zata kara rungumar fasahohin duba kiwon lafiya da zai amfani uwa lokacin da take da juna biyu da kuma bayan haihuwa.