Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying wadda ta bayyana hakan yau Jumma'a yayin taron manema labarai ta ce, kasar Sin tana goyon bayan kasar Kenya a yakin da take da duk wani nau'in manyan laifuffuka.
Ta kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta hada kai da kasar Kenya don ganin an gudanar da bincike yadda ya kamata. Madam Hua ta kuma bayyana fatan cewa, kasar Kenya za ta kare 'yancin Sinawa tare da duba lamarin ta hanyar da ta dace.
Rahotanni na cewa, 'yan sandan Kenya sun kama Sinawan ne bisa zargin zambar satar kudaden jama'a ta hanyar intanet daga wasu gidaje da suke zaune. (Ibrahim)