Abokan hulda na ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Kenya sun kaddamar a ranar Jumma'a da wani sabon shirin dabara na shekaru biya domin bada azama wajen yaki da cutar Sida. Sakataren ma'aikatar kiwon lafiya, James Macharia, ya bayyana cewa tsarin dabara na yaki da cutar Sida a kasar Kenya na shekarar 2014 zuwa 2019 zai bada kwarin gwiwa wajen yaki da annobar ta hanyar fadakar da jama'a, gwajin jini bisa yarda da samar da maganin dake rage kaifin wannan cuta ga kowa. Sabon shirin na bayyana niyyarmu rage zuwa sifiri na wadanda suke dauke da cutar da ma wadanda suka mutu sakamakon Sida. Haka kuma shirin yana maida hankali kan zuba jarin da ya wajaba kan kula da karuwar jama'a in ji mista Macharia a yayin bikin kaddamar da shirin a birnin Nairobi. Kasar Kenya na daya daga cikin kasashe biyar da cutar Sida ta fi shafa a nahiyar Afrika dalilin wasu al'adun kasar da babu kyau misalin gadon mata, auren mata da yawa da rashin fadakar da jama'a a yankuna masu nisa.
A halin yanzu, kasar Kenya na kunshe da mutane kusan miliyan 1.6 dake dauke da cutar Sida, haka kuma gwamnatin kasar nata kokarin gudanar da kamfen fadakarwa domin rage yaduwar cutar a cikin gungun mutanen dake cikin hadari. (Maman Ada)