A jawabin da ya gabatar a wajen bikin da aka yi a jiya Juma'a, wato ranar da kasar ta cika shekaru 51 da samun 'yancin kai wanda ya gudana a birnin Nairobi hedkwatar kasar, shugaba Kenyatta ya yi kira ga al'ummar kasar da kada su manta tarihi, su kuma hada kai da juna, domin tabbatar da ci gaba da wadatar kasar.
Game da matsanancin halin da kasar ke ciki a yanzu haka kuwa, Kenyatta ya yi nuni da cewa, gwamnatin sa ta gabatarwa majalisar dokokin kasar shirin gyaran dokar tsaro, shirin da zai kara ba wa hukumomin tsaron kasar iko, tare da kara sa ido kan 'yan ta'adda, da masu tsatsauran ra'ayi, da ma batun tsaurara hukunci ga wadanda ka iya kawo barazana ga tsaron kasar.
Haka zalika, shugaban na Kenya ya kara da cewa baya ga illar da ayyukan ta'addanci ke haifarwa ga jama'a, su na kuma matukar barazana ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.
Ya ce Kenya za ta habaka karfin tsaron ta, da kuma kara bunkasa amfani da na'urori, da kimiyya wajen kiyaye tsaro. A sa'i daya kuma, ya yi kira ga kasashen duniya da su kara baiwa Kenya taimako ta fuskar yaki da ta'addanci. (Amina)