'yan kungiyar dauke da manyan makamai suka afka ma garin na fotokol da sanyin safiyar laraban nan inda suka kai hari a sansanin soji kuma ya zuwa lokacin wannan rahoton sojojin na kokarin maida martani, ba tare da bada adadin wadanda suka mutu ko jikkata ba.
Harin ta kungiyar Boko Haram dai tazo ne kwanaki uku bayan kokarin da tayi na shiga garin ya ci tura, sojojin kasar da hadin gwiwar na Chadi suka fafutuke su.