Babban magatakardan MDD, mista Ban Ki-moon ya nuna yabo a ranar Asabar kan matakin da kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta dauka na tura sojoji 7500 domin yaki da kungiyar Boko Haram, kungiyar dake ci gaba da janyo tashin hankali da kashe kashe a yammacin Afrika tun yau da 'yan shekaru da dama.
Sakatare janar na MDD ya yaba da wannan mataki a yayin babban taron shugabannin kungiyar AU karo na 24 da aka bude a ranar Jumma'a a birnin Addis Abeba, hedkwatar kasar Habasha. Kwamitin zaman lafiya da tsaro na MDD ya dauki niyya a ranar Alhamis ta ba da amincewarsa kan tura wata rundunar kasa da kasa domin yaki da ta'addanci a yammacin Afrika. (Maman Ada)