Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta Laberiya, ta ce, cutar Ebola ta yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasarta.
Sirleaf ta ce, baya ga tattalin arziki, tasirin cutar ya kuma shafi harkokin kiwon lafiya, da na samar da abinci, kasuwanci da sufuri, da kuma zamantakewar al'umma.
Shugaba Sirleaf ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ta yi da 'yan majalissar kasar.
Da take tsokaci game da alkaluman kididdigar tattalin arziki, Sirleaf ta ce, bullar wannan cuta ya haifar da karuwar ci gaba daga kaso 5.9 bisa dari zuwa kaso 0.4 bisa dari a fannin na tattalin arziki.
Kaza lika shugabar Laberiyan ta ce, ya zama wajibi a gudanar da sauye-sauye ga tsarin tattalin arzikin kasar, muddin ana fatan cimma muradun da aka sanya gaba, a fannonin samar da manyan ababen more rayuwa.
Ta ce, akwai bukatar kara zuba jari a fannonin dake bunkasa tattalin arziki, a kuma gudanar da sauye-sauye a harkokin gudanarwa. (Saminu)