A jiya Asabar ne babban magatakardan MDD Mr. Ban Ki-Moon ta bakin kakakinsa, ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai kan wata mota a yankin Mandela dake arewacin kasar Kenya, tare kuma da bayyana kudurinsa na ci gaba da baiwa kasar Kenya da sauran kasashe a wannan yanki taimako wajen yaki da ta'addanci.
Wani jami'in kasar Kenya ya nuna a wannan rana cewa, wasu masu dauke da makamai ne suka sace wata mota da safiyar wannan rana, a kan hanyarta ta zuwa birnin Nairobi hedkwatar kasa. 'Yan ta'adda sun raba fasinjojin kashi biyu, wato 'yan Somaliya da wadanda ba 'yan Somaliya ba, daga baya suka harbe wadanda ba 'yan Somaliya ba. Wani jami'in 'yan sandan yankin Mandela ya ce, mayakan kungiyar Al-Shabaab ne suka aiwatar da wannan danyen aiki
An ba da labari cewa, yankin Mandela yana kan iyaka tsakanin Kenya da Somaliya, a sha kai hare-hare a wannan yanki da wasu wurare dake gabashin Kenya tun bayan da kasar Kenya ta tura sojinta domin murkushe mayakan Al-Shabaab a shekarar 2011. (Amina)