Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya ce, yana fatan kasashen da ke yankin na Great Lakes, za su fito da wata shawara mai kyau ta hanyar tattaunawa yayin taron don warware matsalar tsaro.
Sakantaren taron Puluosipo Higiro ya furta cewa, wasu mambobin kasashe na matukar fuskantar matsalar tsaro, musamman ma a gabashin Kongon Kinshasa, Afrika ta tsakiya da Sudan. (Amina)