Jakadan kasar Burundi dake kasar Sin ya yi murnar bude tashar rediyon CRI a Bujumbura
A ranar 28 ga wata ne, aka bude tashar FM ta rediyon CRI dake Bujumbura ta kasar Burundi a hukunce, inda za ta rika watsa shirye-shiryensa a kan mita 89.2 na zangon FM. Wannan ita ce tasha ta 15 da ke watsa shirye-shiryen a harshen Faransanci da gidan rediyon CRI ya bude, kana ita ce tashar nahiyar Asiya ta farko da aka bude a kasar Burundi. Jakadan kasar Burundi dake kasar Sin Gasunzu Pascal ya bayyana wa 'yan jarida na CRI cewa, ya yi maraba ga bude tashar rediyon CRI a kasarsa.
Wannan tasha da rediyon CRI ya bude a Bujumbura dake kasar Burundi za ta rike gabatar da shirye-shirye na tsawon sa'o'i 21 cikin harshen Faransanci da kuma sa'o'i 3 cikin karshen Kiswahili a kowace rana, wadanda za su kunshi labarai da sharhi a fannonin tattalin arziki, al'adu, zamantakewar al'umma da dai sauransu. (Zainab)