in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi taron zaman lafiya da tsaro na kungiyar EAC a watan gobe
2013-10-31 10:39:44 cri
A ranar 30 ga wata, ofishin sakataren kungiyar gamayyar gabashin kasashen Afrika ta EAC, ya sanar da cewa, daga ranar 13 zuwa 15 ga watan Nuwamba mai zuwa, za a gudanar da taron zaman lafiya da tsaro karo na biyu, na kungiyar EAC a birnin Bujumbura, hedkwatar kasar Burundi. Taron da ake sa ran jami'an gwamnatoci na kasashe 5, na kungiyar ta EAC, da kwararru, da masana kimanin 150 za su halarta.

Taken taron shi ne "sa kaimi ga yin shawarwari da samun fahimtar juna, don magance rikici, da cimma burin zaman lafiya". Kana taron zai samar da wani dandali ga kasashe mambobin kungiyar, don tattauna batun samar da zaman lafiya a shiyya-shiyya, da matakan da ake dauka, da sakamakon da za a samu wajen magance rikici, da musayar fasahohi daga sauran yankuna.

Bisa labarin da aka samu, an ce mahalartar taron, za su yi nazari, tare da tattauna fasahohin da kungiyar EAC ta samu, da kalubalen da take fuskanta, da matakan da suka dace da ta dauka, don bunkasa shawarwari tsakanin mambobin kungiyar ta EAC, da samun fahimtar juna, da samar da zaman lafiya a tsakaninsu. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China