Wadannan taruruka biyu na da ma'ana matuka, kuma zasu zama tamkar wani mataki dake hada da da nan gaba, game da yadda za a tabbatar da abubuwan da aka cimma a babban taron wakilan jam'iyyar JKS na kasar Sin, yadda za a ci gaba da yin kwaskwarima, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da rage gibin kudin shiga tsakanin jama'a, tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da sauran abubuwa.
Jakadan kasar Burundi dake kasar Sin Pascal GASUNZU ya shedawa wakilinmu cewa, yana da kyakkyawar fata ga wadannan manyan taruka biyu da za a yi.
Pascal GASUNZU ya mai da muhimmanci sosai kan tarurukan biyu. A ra'ayinsa, mika mulki da shugabannin kasar ta Sin za su yi, zai kawo babban tasiri ga manufofin da Sin za ta dauka nan gaba. Ya ce, ba jama'ar kasar Burundi ne kadai ke maida hankali kan tarurukan biyu ba, har da ragowar dukkan alummomin duniya, haka duniya tana jiran sakamako mai kyau da za a samu a cikin tarurukan.
Bugu da kari, Pascal GASUNZU ya ce, kafofin yada labaru na kasar, suna mai da hankali sosai kan tarukan, kuma labarai makamantan wannan daga kasar Sin, na da muhimmanci sosai ga kasar Burundi wadda take kokarin farfadowa da tallafin kasar ta Sin.
A kalaman Pascal GASUNZU, akwai bukatar cimma nasarar da aka sanya gaba, yayin gudanar da tarukan biyu, kuma yayi imani da cewa za a samu ci gaba mai kyau. Bugu da kari, yana fatan nan gaba kasashen biyu za su kara cimma yarjeniyoyi a fannoni daban-daban, tare kuma da kara habaka hadin kai tsakanin kasashen biyu, matakan da za su yi amfani matuka ga karfafa dankon zumunci dake tsakanin su a nan gaba. (Amina)