Ofishin WHO ya ce har ya zuwa yanzu kasashen Guinea, da Liberia, da Sierra Leone, na ci gaba da fuskantar matsaloli masu alaka da yaduwar cutar ta Ebola.
Hakan dai na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da kasar Sierra Leone ta sanar da soke umurnin sa ido kan cutar a dukkanin fadin kasar.
WHOn ta ce akwai karancin kudi da ake kashewa wajenbukata da ma biyan masu aikin jiyya, kana mai yiwuwa ne zuwan yanayin damina, ya kara haifar da koma baya ga wannan aiki.
Mataimakin babban darekta mai kula da aikin dakile yaduwar cutar ta Ebola hukumar ta WHO Bruce Aylward, ya shaidawa wani taron manema labaru cewa, a 'yan makwannin da suka gabata, yaduwar cutar ya yi ragu a kasashen Guinea, da Liberia, da kuma Sierra Leone. Sai dai duk da haka ana bukatar karin kudade da suka kai dala miliyan 350, domin ci gaba da yaki da cutar ta Ebola.(Fatima)