Taron wanda ake sa ran gudanarwa daga ranar 23 ga watan Fabrairu a Abidjan,babban birnin kasar Ivory Coast, zai samu halartar ministocin harkokin kasashen waje,shari'a da na cikin gida na kasashen yammacin Afirka da kuma manyan wakilan kungiyoyin ECOWAS,AU,kungiyar musulmi ta duniya da kungiyar kasashen kogin Mano.
Manufar taron ita ce, tattauna batun rashin kasar asali da nufin gano mutanen da suka fada wani irin hali,tsara matakan kare su,bullo da hanyoyin hana abkuwar lamarin da rage matsalar kasar asali da ake fuskanta a shiyyar.
Wata sanarwa na nuni da cewa,gwamnatin kasar Cote d'Ivoire tare da hadin gwiwar UNHRC da ECOWAS ne suka dauki nauyin shirya wannan taro.
Bayanai na nuna cewa, cikin mutane miliyan 10 da ba su da kasar su ta asali ko suke fuskantar barazanar rasa kasar su ta asali a duniya, a kalla mutane 750,000 daga cikinsu na zaune ne a yammacin Afirka,kuma wannan matsala na kai ga mutum iya rasa kasar asali har ma da muhimman abubuwan da suka shafi 'yancin dan-adam.(Ibrahim)