in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Catherine Samba-Panza ta nada Mahamat Kamoun, a matsayin sabon fraministan kasar
2014-08-11 11:00:05 cri

Kamfanin dillancin labarai na Jamhuriyar Africa ta Tsakiya, ya ce shi dai Mahamat Kamoun ya maye gurbin tsohon firaminista Andre Nzapayeke.

Tsohon firaministan, Nzapayeke, wanda kwararre ne a fannin tattalin arzikin kasa, a da yana aiki ne da bankin raya kasashe na Africa a matsayin babban sakataren bankin, to amma ya sabka daga mukaminsa domin yin biyayya ga sharuddan yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce aka amince da ita tsakanin kristoci da bangarorin musulmai 'yan adawa a ranar 23 ga watan Yuli.

Yakin basasa ya barke a kasar ta Jamhuriyar Africa ta Tsakiya, a ranar 10 ga watan Disamba na shekarar 2012, tsakanin kungiyar 'yan adawa ta Seleke da kuma dakarun rundunar gwamnatin kasar. Kungiyar Seleke ta kwace mulkin kasar daga hannun tsohon shugaban kasar na wancan lokacin Francois Bozize, a watan Maris na shekarar 2013, kuma shugaban 'yan tsageren Seleke Michel Djotodi, ya yi shelar cewa shi ne sabon shugaban kasar, hakan ya tabbata a yayin majalisar mika mulkin ta kasar, an nada shi a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya.

To amma kuma a watan Janairun shekarar 2014 da muke ciki, sai tilas tasa shugaba Djotodia, ya sabka daga kan mukaminsa a yayin da rikici ya kazanta tsakanin kristoci 'yan balaka da musulmai 'yan seleke. To a kuma daidai wancan lokacin ne sai majalisar mika mulki ta kasar ta zabi Catherine Samba-Panza, a matsayin shugaba ta rikon kwarya. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China