in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sallami jami'an 'yan sanda 70 a Afrika ta Kudu bisa laifin cin hanci
2014-07-09 20:37:14 cri
A cigaba da take yi na yaki da cin hanci a kasar Afrika ta Kudu jami'an 'yan sanda 70 ne suka fada tarkon gwamnatin a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar laraban nan.

Sanarwar Gwamnatin da aka fitar tayi bayanin cewa an dai sami jami'an 'yan sandan ne da laifin cin hanci da rashawa,yunkurin kissan kai,fashi da makami,take umurnin shari'a da cin zarafi.

Gwamnati dai ta sha alwashin kakkabe duk wani ayyukan cin hanci da muggan tabi'u ta hanyar kafa wata hukuma na bincike wanda shi ne ya fidda sakamakon da yayi sanadin sallamar wadannan jami'an 'yan sanda bisa laifin cin hancin.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China