Muhammad Carmon ya fadi hakan ne a zantawar sa da manema labaru a kwanan baya inda ya bayyana cewa shawarwari zai baiwa dukkan al'umma wata dama mai kyau wajen daidaita bambancin ra'ayi dake tsakaninsu.
Firaministan wanda lurar da cewa ta haka ne kasar za ta samun farfadowa sai dai bai tabbatar da hakikkanin lokaci da hanyar da za a bi wajen yin shawarwarin ba.
An ce bangarorin biyu dake dauki ba dadi tsakaninsu wato dakarun sojin sa kai na Anti-Balaka da tsohon kungiya mai adawa da gwamnati ta Seleka sun kai ga matsaya daya na dai na zaman gaba a tsakanin su a birnin Brazzaville a ran 23 ga watan Yuli, sakamakon haka ne suka nemi a yi shawarwari tsakanin al'umma.
Bisa wannan yarjejeniyar da suka cimma, shugabar kasar ta wucin gadi Catherine Samba-Panza ta nada Carmon a matsayin sabon firaministan wucin gadi na kasar. (Amina)