Binciken kimiyya, fasaha da ilimin lissafi da bincike a fannin injiniya sun lunka nunka sau biyu a tsawon shekaru goma na baya bayan nan kana ingancinsu ya karu sosai, amma kuma ba sa isa domin tallafawa tattalin arzikin Afrika dake karuwa cikin sauri in ji Makhtar Diop, mataimakin shugaban bankin duniya reshen Afrika. Ya kamata mu kara karfin mu na yin bincike na zamani dake maida hankali a bangaren masana'antu ta yadda tattalin arzikin Afrika zai fi kasancewa na takara, har ma kuma da karfafa hulda tsakanin kasashe a wajen neman hanyoyin cimma mafita na hadin gwiwa dake dogaro kan binciken kalubaloli na yanzu mafi gaggawa na cigaba in ji mista Makhtar. (Maman Ada)