Afrika ta Kudu ce kadai kasar Afrika da take cikin kungiyar G20.
Shugaba Jacob Zuma zai jagoranci tawagar kasar sa zuwa taron a birnin Brisbane na kasar Australia daga ranakun 13-16 ga watan nan inji kakakin fadar gwamnati Mac Maharaj.
Shugabannin G20 zasu tattauna tattalin arzikin duniya sakamakon wata farfadowar da ta yi mara karfi.
Traon zai mai da hankali kuma a kan yadda kasashen G20 gaba daya da kowannen su za su dauki Karin mataki domin daga cigaban tattalin arzikin duniya ta fidda tsarin da zai daga GDPn da fiye da kashi 2 cikin 100 a cikin shekaru 5.
Haka kuma ana sa ran Shugabannin BRICS za su gana da junan su a bangaren wannan taron na G20. ganawar zai bada dama ga shugabannin kasashen na BRICS da su waiwaya cigaban da aka samu a kan aiwatar da yarjejeniyar Fortaleza na 2014,musamman ganin ya jibanci sabon bankin cigaba da cibiyarsa a yankin Afrika.(Fatimah Jibril)