Mutane biyu su rasa rayukansu ya yin barkewar wani fada a yankin Soweto dake birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, sakamakon wata rashin jituwa da ya auku tsakanin mazauna yankin da wasu baki 'yan kasar waje.
Rahotanni sun bayyana cewa tun da fari wani dan kasuwa bako ne ya harbe wani matashi dan kasar da bindiga a ranar Litinin din da ta gabata,matashin da yake yunkurin satar kaya a shagonsa, lamarin da ya sanya al'ummar wurin kashe wani bako daya a matsayin ramuwar gayya, tare da wawashe kantuna kusan 100.
Kakakin 'yan sandan kasar Afrika ta kudun ya shaidawa manema labaru a jiya Jumma'a cewa, tuni aka aike da 'yan sanda yankin da rikicin ya auku domin tabbatar da tsaro, tare kuma da aikin lalubo wadanda ke da hannu cikin aukuwar tashin hankalin.
A wani ci gaban kuma, fadar gwamnatin kasar ta fidda wata sanarwa dake cewa shugaba Jacob Zuma wanda ke halartar taron Davos a Switzerland, ya umurci hukumomin tsaron kasar da su dauki matakan da suka wajaba, domin dakile rikicin. (Amina)