Wadannan shawarwari na cikin sanarwar karshe ta taron kwamitin kasashe goma na tarayyar Afrika kan batun yi wa MDD gyaran fuska da ya gudana a ranar Jumma'a Oyo, birnin da aka haifi shugaban kasar Congo, Denis Sassou N'Guesso, mai tazarar kilomita 400 daga arewacin birnin Brazzaville.
Dandalin da kasar Congo ta shirya a karkashin shugaban kwamitin, shugaban kasar Sierra-Leone Ernest Bai Koroma tare da taimakon takwarorinsa na kasashen Congo, Guinee-Equatoriale, shugaban kwamitin kasa na Libya, ministocin harkokin wajen kasashe shida da kuma kwamishinonin harkokin siyasa na tarayyar AU.
Makasudin da ake son cimma shi ne Afrika, ta samu 'yancin wakilta a cikin manyan hukumomin gudanarwa na MDD, musamman ma a kwamitin sulhu. Cikin tarihi, Afrika ita ce shiyya kadai a duniya da bata da wakilci a cikin mambobi na dinidindin a kwamitin sulhu na MDD in ji sanarwar karshe ta Oyo. (Maman Ada)