Ministan ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke jawabi a wani taron karawa juna sani kan yadda za a aiwatar da wannan yarjejeniya wanda aka shirya tare da hadin gwiwar kungiyar kwadago ta duniya ILO.
Ya ce, yarjejeniyar za ta taimaka wajen samar da yanayin aikin da ya dace, wurin kwana, nishadantarwa, abinci da kuma yanayin kiwon lafiya mai inganci.
Don haka, ministan ya bukaci kasashe mambobin kungiyar, kungiyar kasashen raya tattalin arzikin tsakiyar Afirka(ECCAS) da su bullo da matakan sa-ido kan 'yancin amfani da iyakokin ruwayensu.
Taron karawa juna sanin na kwanaki hudu ya hallara kan kwararru daga kungiyar ILO da kasashe mambobin ECCAS wadanda suka hada da Jamhuriyar Congo,Gabon,Jamhuriyar Afirka ta tsakiya,Chadi,Kamaru,Equatorial,Guinea,Jamhuriyar demokiradiyar Congo da kuma Angola.(Ibrahim)