Wata sanarwar da aka bayar a Nairobi jim kadan kafin tashin shugaba Kenyatta zuwa Amurka, ta ce shugaban kasar na Kenya zai gana da wasu gungun 'yan kasuwa na kasar Amurka wadanda ke da sha'awar saka jari a kasar ta Kenya.
Wannan taron koli wanda hukumomin kula da cinikayya na kasashen biyu sun shirya shi ne domin jawo hankalin saka jari a kasar Kenya daga kasashen ketare.
Sanarwar ta ce Kenyatta zai halarci taron koli na Amurka da shugabannin kasasshen Africa domin tattaunawa a kan ci gaba mai dorewa da kuma saka jari mai tabbatar da kyakkyawar makomar Africa, zaman lafiya da tsaro.
Wata kididdiga da aka fitar a kasar Kenya a kwanan nan ta nuna cewar cinikayya tsakanin Kenya da Amurka ta kai darajar kudi har fiye da dalar Amurka biliyan daya da miliyan dari 1 a shekarar 2013.
Kasar Kenya na da niyyar kara kaimi wajen neman Amrka ta sabunta yarjejeniya cinikayyar tsakanin Amurka da kasshen Africa na shekaru 15 masu zuwa tare da daddale matsaloli da suka shafi cinikayyar. (Suwaiba)