Shugaba Jonathan wanda ya bayyana hakan a filin taro na Eagles Square dake birnin tarayyar kasar Abuja, ya ce ya yanke shawarar sake tsayawa takarar ne domin amsa bukatar dinbin magoya bayan sa.
Bayan zayyana jerin ayyukan da ya ce gwamnatin sa ta aiwatar, Jonathan ya bukaci daukacin al'ummar Najeriya su mara masa baya domin ya samu damar kammala ayyukan da ya fara tun daga 2011 kawo wannan lokaci.
Taron gangamin magoya bayan shugaban mai ci dai ya samu halartar dubun dubatar 'yan jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, da jagororin al'umma, da gwamnoni da sauran magoya baya.
Kafin hakan dai a ranar 30 ga watan Oktobar da ya gabata shugaba Najeriyar ya yanki katin neman takarar ta sa daga ofishin jam'iyar sa ta PDP, a matsayin dan takara daya tilo da jam'iyyar ta amince da shi. (Saminu Alhassan)