Da yake karin haske game da hakan, babban sifeton 'yan sandan kasar Suleiman Abba, ya bayyana takaicin yadda a cewarsa wasu daga 'yan majalissun dokokin suka hana jami'an 'yan sanda gudanar da aikinsu.
Abba wanda ya bayyana wa manema labaru hakan, jim kadan da kammala ganawa da mataimaka shugaban kasar Namadi Sambo, ya kuma yi watsi da zargin da aka yi wa 'yan sandan, na hana 'yan majalissar ta wakilai gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta tanada.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Alhamis din da ta gabata ne, wasu 'yan majalissar wakilan Najeriyar suka haura kyauren majalissar, bayan zargin 'yan sanda da garkame kofa. Kafin daga bisani shugaban majalissar dattijan kasar David Mark, ya sanar da rufe majalissun dokokin ya zuwa ranar Talata. (Saminu Alhassan)