Mujallar harkokin zuba jari a Afrika wato "Ventures Africa" ta gabatar da jerin sunaye mawadata 'yan Afrika na shekarar 2014, jadawalin da ya nuna cewa akwai 'yan Afrika 55 dake da kudi da yawansu ya haura dala miliyan dubu 1, adadin da mujallar ta ce ya yi daidai da na shekarar bara.
Bisa labarin da ta fitar, yawan dukiyoyin wadannan mutane 55, ya kai dala biliyan 161.75, yayin da yawan kudin 'yan Najeriya cikin wannan adadi ya kai kashi 48 cikin dari, ciki hadda hamshakin dan kasuwar nan na Najeriyar Aliko Dangote, da ke ci gaba da rike matsayin mutum mafi yawan dukiya a nahiyar.An ce yawan dukiyar Aliko Dangote ta kai dala biliyan 25.7.
A nasu bangaren 'yan kasuwar Afrika ta kudu sun mallaki dukiyar da ta kai dala biliyan 32, kimanin kashi 20 cikin dari na daukacin wanccan jimilla ke nan. (Amina)