A ran 13 ga wata bisa agogon New York, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya sanar da karbar takardar yin murabus daga manzon musamman na MDD da kungiyar kawancen kasashen Larabawa da ke kula da rikicin Sham Lakhdar Brahimi, inda Ban Ki-Moon ya nuna bakin cikinsa, Brahimi zai gama wa'adin aikinsa a ranar 31 ga watan Mayu. Ban da wannan kuma, game da wanda zai maye gurbin Brahimi, Ban Ki-Moon ya yi nuni da cewa, yana bukatar lokaci domin ya yi la'akari da mutumin da ya dace da wannan mukami.
Brahimi ya maye gurbin tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan, inda ya zama manzon musamman na MDD da kawancen kasashen Larabawa kan rikicin Sham a watan Agusta na shekara ta 2012. A cikin wa'adin aikinsa na kusan shekaru 2, wannan babban jami'in diplomasiyya ya gudanar da aikin samun sulhuntawa cikin yakini, kana ya shirya taron duniya na Geneva don daidaita matsalolin Sham cikin nasara. Ban Ki-Moon ya yaba kokarin da Brahimi ya yi a cikin sanarwar, amma a sa'i daya kuma, ya nuna cewa, kokarin da Brahimi ya yi bai samu cikakken goyon baya na gaskiya daga bangarorin da abin ya shafa ba, wannan koma baya ce ga kowa da kowa. (Danladi)