Da misalin karfe 7 na safiyar ranar 3 ga wata bisa agogon wurin, an fara kada kuri'ar babban zabe a kasar Sham a hukunce.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Sham, ta bayyana cewa adadin masu kada kuri'a a duk fadin kasar ya kai miliyan 15.84, kuma an kafa rumfunan zabe dubu 9.6 a duk fadin kasar, masu zabe na iya kada kuri'unsu a ko wace tasha tare da katin shaida.
Zaben na wannan karo na gudana a yayin kasar ke fama da matsala, wanda ya hada 'yan takara uku wato shugaban kasar mai bari gado Bashar al-Assad, 'dan majalisar dokoki Maher al-Hadschar da tsohon ministan kasar Hassan al-Nuri. Masu nazari suna ganin cewa, Bashar al-Assad zai lashe wannan zabe da babban rinjaye. (Danladi)