Shugabannin kasashe kungiyar G7 sun ba da wata sanarwar hadin gwiwa dangane da batun Ukraine a jiya ranar Jumma'a 13 ga wata, inda suka nuna cewa, dukkansu da kuma shugaban kwamitin Turai da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Turai sun yi maraba da sabuwar yarjejeniyar Minsk. Suna ganin cewa, yarjejeniyar za ta samar da kyakkyawar makoma wajen lalubo hanyar wanzar da dauwamammen zaman lafiya a gabashin kasar Ukraine daga dukkan fannoni.
A wannan rana kuma, gwamnatin kasar Jamus ta bayar da wannan sanarwa a shafinta na Intanet. A cikin sanarwar, shugabannin kungiyar G7 sun yi kira ga sassa daban daban da su bi yarjejeniyar ta Minsk yadda ya kamata, su dauki matakan da aka tsara nan da nan ba tare da bata lokaci ba, sa'an nan su tsagaita bude wuta a ranar 15 ga wata. Nan da kwanaki da dama masu zuwa, kamata ya yi sassa daban daban su daina matakan da za su hana tsagaita bude wuta a tsakaninsu. Har wa yau kuma, idan bangarori masu ruwa da tsaki su saba wa yarjejeniyar ta Minsk, musamman ma a fannonin tsagaita bude wuta daga dukkan fannoni da kuma daina amfani da manyan makamai, kungiyar G7 a shirye take wajen daukar matakan da suka wajaba kan bangarorin daban daban da wannan rikici ya shafa.
Haka zalika sanarwar ta ce, kungiyar G7 ta yi maraba da rattaba hannu kan yarjejeniyar ba da taimako a tsakanin asusun ba da lamuni na duniya wato IMF da gwamnatin kasar Ukraine. (Tasallah)