A ranar, bangarorin uku sun gudanar da shawarwari cikin sirri a birnin Minsk, inda suka cimma wasu muhimman yarjejeniyoyi dangane da yadda sassa masu rikici da juna a gabashin Ukraine za su janye manyan makamansu, da tsarin da za a bi wajen tsagaita bude wuta, da kuma yadda za a sa ido a kan tsagaita bude wutan. Har wa yau, a labarin da kamfanin dillancin labarai na kasar Belarus ya bayar, an ce mahalarta taron sun kuma tattauna matsayin gabashin Ukraine da kuma batun gudanar da zabe a wurin.(Lubabatu)