Bai kamata a mayar da yunkurin warware matsalar Ukraine ta hanyar siyasa baya ba, in ji Sin
Dangane da dukkanin matakan da bangarorin da abin ya shafa suka dauka domin warware rikicin Ukraine, yau Litinin 9 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying ta bayyana a birnin Beijing cewa, kasar Sin na maraba da dukkanin matakan da aka dauka domin sassauta halin da ake ciki da kuma warware rikicin gabashin kasar Ukraine ta hanyar siyasa, haka kuma ta bukaci bangarorin da abin ya shafa da kada su dauki matakan da za su rura wutar rikicin kasar Ukraine da kuma duk wani matakin da zai haddasa illa ga yunkurin warware matsalar kasar ta hanyar siyasa, kana kasar Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa domin ciyar da kokarin da ake na warware matsalar kasar gaba.
Bugu da kari, Hua Chunying ta jaddada cewa, a halin yanzu, abu mafi muhimmanci ga jama'ar yankin gabashin kasar Ukraine shi ne samun kwanciyar hankali a maimakon makamai. (Maryam)