Da yake tsokaci game da wannan batu, shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin, ya ce hukumomi a Ukraine sun ki amincewa da hanyar warware rikicin yankin Donbass ta hanyar siyasa, kana ta yi amfani da damar tsagaita bude wuta wajen sake daura damarar yaki.
A nasa bangare shugaban kasar Ukraine Petro Poroszenko, ya ce akwai bukatar daukar hakikanin matakan amfani da gudummawar jin kai, da ake samarwa jama'ar yankunan gabashin kasar Ukraine, ba wai irin gudummawar jabu, da kasar Rasha ke shirin kaiwa karo na 12 zuwa yankin Donbass ba, kayayyakin da a cewar Ukraine makamai ne da Rashan ke baiwa 'yan ta'adda.
Game da hakan, zaunannen wakilin Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kaiwa fararen hula.
Mr. Liu ya ce, tsanantar halin da ake ciki a yankin gabashin kasar Ukraine, bai dace da moriyar dukkanin sassa ba. Ya ce aikin da ya fi kowanne muhimmanci shi ne kwantar da hankali, da magance kara tsanantar rikicin, da tsagaita bude wuta cikin hanzari a yankin, da kuma aiwatar da yarjejeniyar Minsk, da aka cimma a watan Satumbar bara. (Zainab)