Manyan batutuwan dake kunshe cikin yarjejeniyar sun hada da, dakatar da musayar wuta a gabashin kasar Ukraine a ran 15 ga wata, da kuma janye manyan makamai daga wuraren da ake kai hare-hare da dai sauransu.
Bugu da kari, Mr.Putin ya bayyana cewa, tawagar bangarori uku kan batun na Ukraine da suka hada da kasar Ukraine, kungiyar tsaro da hadin gwiwa ta Turai da kuma kasar Rasha sun kuma kulla wata yarjejeniya don ganin an aiwatar da abubuwan da ke kunshe cikin yarjejeniyar Mensk da aka sa hannu a watan Satumba na shekarar 2014 da ta gabata yadda ya kamata. (Maryam)