Obama ya bayyana hakan ne ya yin ganawarsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a jiya Litinin a fadar sa ta White House.
Da take maida jawabi Merkel ta jaddada cewa, a hanlin da ake ciki babu wani shiri na amfani da ayyukan soji wajen warware rikicin kasar ta Ukraine, don haka kamata ya yi bangarorin da wannan batu ya shafa, su kara azama wajen warware sabanin ta hanyar diplomasiyya.
Ganawar shuwagabannin biyu dai na zuwa ne a gabar da shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin ke fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Masar, inda kafin tashin sa zuwa Masar din ya bayyana cewa, ba za a iya warware rikicin kasar Ukraine ba, har sai dukkanin bangarorin kasar ta Ukraine su yi watsi da tsattsauran ra'ayi da kuma kabilanci.
Kaza lika shugaba Putin ya yi kira ga kasashen duniya da su bada gudummawa wajen sa kaimi ga bangarorin biyu, game da batun komawa teburin shawarwarin shimfida zaman lafiya. Ya ce Rasha za ta ci gaba da jan hankalin mahukuntan kasar Ukraine, da ma mayakan sa kai dake gabashin kasar wajen amincewa ga bukatar gudanar da shawarwari kai tsaye.
A wani ci gaban kuma, taron ministocin harkokin wajen kasashe membobin kungiyar EU da ya gudana a jiya Litinin, ya amince da kara saka takunkumi ga bangarorin da rikicin kasar Ukraine ya shafa, koda yake taron ya amince da samar da damar shiga tsakanin bangarorin.
Har wa yau mahalarta taron sun tsaida kudurin jinkirta kakaba takunkumi ga dakarun dake gabashin kasar ta Ukraine, da kuma kasar Rasha, ya zuwa ranar 16 ga wannan wata da muke ciki. (Zainab)