A yayin wannan lokaci mutane kasar sun yi shiru na tsawon minti daya a ranar 25 ga wata da misalin karfe goma sha biyu na rana domin nuna juyayinsu ga mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da aka kai a kasar ta Ukraine. A wannan rana, dukkan ma'aikatun gwamnati, hukumomi, da kamfanonin mallakar kasar sun sauko da tutar kasar kasa domin nuna juyayi, tare kuma da soke duk wasanni da bukukuwa a duk fadin kasar, haka kuma gidajen rediyo da telebijin sun rika gudanar da shirye-shiryen musamman a wannan rana.
Hakazalika kuma, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya buga wayar tarho ga sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry a wannan rana, inda Lavrov ya yi kira ga kasar Amurka da ta yi matsin lamba ga kasar Ukraine don warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar yin shawarwari ba amfani da karfin soja ba. Jami'an biyu su ma sun cimma daidaito kan cewa, kamata ya yi bangarori biyu dake rikici da juna a Ukraine su kawo karshen kai hare haren boma-bomai a yankin Donbass, tare da janye manyan makamai daga filin daga. Mista Lavrov ya bayyana cewa, samun ci gaba kan warware rikicin Ukraine yana dogaro ne da niyyar gwamnatin kasar Ukraine ta yin shawarwarin kai tsaye tare da 'yan a-waren gabashin kasar. (Zainab)