Kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da taro kan batun Ukraine a wannan rana, inda Liu Jieyi ya yi jawabi cewa, a kwanakin baya an fuskanci rikice-rikice a yankin gabashin kasar Ukraine, kana yanayi ya tsananta a yankin, wanda ya haddasa asarar rayuka da raunatar mutane da hasarori da dama. Kasar Sin ta nuna damuwa da kulawa game da wannan lamarin. Sin tana maraba da bangarori daban daban da abin ya shafa da su yi kokarin sa kaimi ga warware batun Ukraine ta hanyar siyasa, kuma Sin tana fatan bangarorin za su yi kokari tare don hanzarta warware batun ta hanyar siyasa a dukkan fannoni na dogon lokaci bisa tsarin shiga-tsakani na Normandy da Minsk bisa la'akari da moriyar juna, wannan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da bunkasuwa a kasar Ukraine da ma yankin baki daya. (Zainab)