Shugaban kasar Ukraine Petro Poroszenko ya bayyana a ranar 12 ga wata cewa, ba cikin sauki ba aka cimma wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, wannan ya nuna alamar cewa, za a fuskanci mawuyacin hali wajen aiwatar da yarjejeniyar a nan gaba.
Shi kuma shugaban kasar Faransa François Hollande cewa ya yi, taron ya kawo kyakkyawar makoma wajen warware rikicin Ukraine, sannan yanzu aiki mafi muhimmanci shi ne yadda za a aiwatar da yarjejeniyar.
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa ta hanyar kakakinsa a wannan rana, inda ya yaba wa shugabannin kasashen hudu da su cimma irin wannan muhimmiyar yarjejeniyar, kana ya kalubalanci bangarori daban daban na kasar Ukraine da su bi yarjejeniyar da tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci.
Ita ma fadar shugaban kasar Amurka wato White House ta bayar da sanarwa a wannan rana, inda ta yi maraba da cimma yarjejeniyar, tana mai fatan cewa, cimma yarjejeniyar shi ne mataki mai muhimmanci wajen warware rikicin kasar Ukraine cikin lumana. A wannan rana kuma, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta bayyana cewa, yanzu ba a tsaida kudurin janye takunkumin da aka yiwa kasar Rasha ba. (Zainab)