Lavrov ya ce, kasar Rasha tana tsayawa tsayin daka wajen warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar zaman lafiya, tana fatan bangarorin biyu da rikicin kasar Ukraine ya shafa su janye manyan makamansu, sabo da ci gaban hare-hare ba za su iya warware rikicin da kasar take fama da shi ba. Ya kuma yi kira ga bangarorin biyu da abin ya shafa da su yi shawarwarin kai tsaye, haka kuma, ya bayyana cewa, za a ci gaba da yin shawarwari kan warware rikicin kasar Ukraine, domin muna ganin cewa, mai iyuwa ne za a iya samun dabarar warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar yin shawarwari.
Bugu da kari, Mr. Lavrov ya ce, wasu kasashen yammacin duniya na ci gaba da zargin kasar Rasha kan rikicin Ukraine, sun kuma yi musu kan moriyar Rasha, amma, cikin ko wane matakin ricikin kasar Ukraine, kasar Amurka da wasu abokanta sun dauki matakan hura wutar rikicin kasar Ukraine. (Maryam)