Dangane da lamarin, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa ta bakin kakakinsa a ran 24, inda ya nuna cewa, bude wuta kan unguwar jama'a ya sabawa dokar jin kai ta kasa da kasa. A sa'i daya kuma, ya yi alla wadai da shugabannin kungiyoyin dakarun kasar Ukraine, domin janyewarsu daga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a ran 23 ga wata, da kuma bukatunsu da ba su dace ba na mamaye karin yankunan kasar, lamarin da ya keta alkawarin da suka cimma cikin yarjejeniyar Minsk.
Bugu da kari, Ban Ki-moon ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su dukufa domin farfado da yarjejeniyar Minsk. Ya kuma jaddada cewa, tsaro, cikakken yankunan kasa da kuma zaman karko na kasar Ukraine su ne tushen tabbatar da tsaro da kuma zaman karko a yankin, ya kamata a farfado da zaman lafiya a kasar Ukraine ba tare da bata lokaci ba. (Maryam)