Bisa labarin da aka samu, an ce, bayan da aka daidaita ma'anar matalautan da za a taimakawa wato wadanda albashinsu bai kai kudin Sin Yuan 1700 ba ya karu zuwa Yuan 2300, yawan matalauta a jihar ta Tibet ya karu zuwa dubu 833, adadin da ya kai kashi 34.42 cikin 100 bisa na duk makiyayan jihar ta Tibet, wanda hakan ya nuna cewa, yawan matalauta a jihar ya kai matsayin koli a duk fadin kasar Sin. Sakamakon tsananin sanyi, da karancin iskar shakawa, kana da manyan tsaunuka, aikin kawar da talauci a jihar Tibet na da wuya ainun.
Direktan ofishin kawar da talauci na jihar Tibet mai cin gashin kanta, Qu Ni Yangpei, ya bayyana cewa, bisa yanayin sarkakkiya da ake ciki wajen kawar da talauci a jihar, jihar Tibet za ta kokarta don lalubo wata hanyar kawar da talauci ta musamman. Haka kuma, za a bi gida-gida don taimakawa matalauta da kyautata zaman rayuwarsu. Ya ce, yanzu an rage yawan matalauta da adadin da ya kai dubu 130, kuma yawan matalauta da ake samu a jihar Tibet ya ragu zuwa dubu 583 (Bako)