Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam, Hua Chunying ce ta bayyana hakan a yau Litinin yayin wani taron manema labarai.
Ta ce kasar Sin ba ta goyon wata kasar waje ta yi amfani da batun Tibet ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta. Tana mai cewa, kasar Sin ba ta taba martaba wa ba kuma ba za ta yi hakan koda a nan gaba ba kan batun wai nada wata jami'a ta musamman kan batun yankin Tibet da kasar Amurka za ta yi,
Rahotanni na cewa, a ranar Jumma'a ce, Amurka ta nada jami'ar ta mai kula da harkokin da suka shafi hakkin bil-adama Sarah Sewall a matsayin jami'a ta musamman mai kula da harkokin yankin Tibet na kasar Sin. (Ibrahim)