Mataimakin sakataren kwamitin birnin Lhasa na jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma shugaban sashin kula da hadin gwiwar jama'a Dawa, wanda ya halarci taron tattaunawar, ya ce, idan aka waiwayi baya a tsawon shekaru 54 da suka gabata, za a gano cewa, da kyar aka kai ga cimma nasarorin da aka samu yanzu, sabo da haka, kamata ya yi a yi farin ciki da abin da ya faru. Ya ce a halin da ake ciki yanzu, musamman yayin da ake sanya wani sabon buri gaba, kamata ya yi a nace ga bin manufa, da inganta hadin gwiwa da ke tsakanin al'ummar yankin, don kokartawa wajen gina birnin Lhasa.(Bako)