in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kura-kuran da ta yi game da yankin Tibet
2014-02-23 16:47:49 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Qin Gang, ya bukaci kasar Amurka da ta gyara kara-kuran da ta tabka, bayan da shugaba Obama ya gana da Dalai Lama.

Qin Gang ya yi wannan kiran ne ranar Asabar cikin wata sanarwar da aka raba wa manema labarai, inda ya ce kamata ya yi Amurka ta dakatar da nuna goyon baya tare da hada bakin da take yi da masu kawo baraka ga kasar Sin, matakin da ya ce yana iya kara lalata dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka.

Ya ce Tibet yanki ne na kasar Sin, kuma batun yankin Tibet batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda bai kamata ba Amurka ta tsoma baki a ciki.

Qin Ganga ya ce, abin da Amurka ta yi na barin Dalai Lama ya ziyarci kasar har ma ya gana da shugaba Obama, duk da kin amincewar kasar Sin, wannan kadai ya isa ya yi mummunar illa ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ya ce, sanin kowa ne cewa, Dalai Lama dan gudun hijirar siyasa, yana fake wa da addini ne da nufin kawo baraka ga kasar Sin.

Tun lokacin da aka 'yantar da yankin Tibet cikin lumana shekaru 60 da suka gabata, yankin na Tibet ya samu gagarumin canje-canje daga dukkan fannoni. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China