A ranar 25 ga wata ne, aka bayyana yanayin tattalin arzikin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, shugaban jihar Losang Gyaltsen ya jadadda cewa, ya kamata a karfafa ayyukan kiyaye muhallin halittu yayin da ake raya tattalin arziki. Ya kuma kara da cewa, ko kusa jihar Tibet ba za ta shigar da na'urori masu amfani da makamashi da dama, gurbata muhalli da kuma masu sarrafa shara da yawa ba, ta yadda za a iya kiyaye gonakin jihar, tsabtace ruwan koguna da ruwan dake karkashin kasa, ta yadda za a kaucewa haddasa bala'un da suka shafi labarin kasa masu tsanani a jihar sakamakon abubuwan da dan Adam ke aikatawa.
Bugu da kari, bisa labaran da aka samu, cikin farkon rabin shekarar bana, an kammala ayyukan tsara shirye-shiryen dasa itatuwa da ciyayi a bakin kogin Lasa, gina hanyoyin zamani a garin Lalin da kuma gina hanyoyin zamani a filayen jiragen sama guda biyar. Kuma fadin filin itatuwa da ciyayi da aka dasa bishiyoyi a jihar ya kai muraba'in kilomita 66273, kuma koguna da iska a jihar na da inganci mai kyau. (Maryam)